News
Ƴan Sanda Sun Damke Ango Da Abokansa Bayan Mutuwar Amarya A Jigawa
Rundunar ƴan sanda ta jihar Jigawa ta cafke mutum huɗu, ciki har da wani ango, Auwal Abdulwahab, mai shekara 20, bisa zargin hannu a mutuwar amaryarsa a ƙaramar hukumar Sule Tankarkar.
LEADSHIP ta ruwaito cewa Lamarin ya faru ne da daren Asabar, inda ake zargin ango tare da wasu abokansa uku — Nura Basiru, Muttaka Lawan, da Hamisu Musa, dukkansu mazauna ƙauyen Tungo — da tilasta wa amaryar yin jima’i da su. A cewar rahotannin, amaryar ta rasu yayin ƙoƙarin tursasa mata hakan.
Gwamnatin Kano Ta Bankado Ma’aikatan Bogi 247, Ta Karɓo Sama Da Naira Miliyan 27
Bayan samun rahoton, jami’an ‘yan sanda suka garzaya wurin inda suka ɗauki gawar mamaciyar zuwa Asibitin Ƙwararru na Gumel. Likitan da ya duba ta ya tabbatar da rasuwarta, kuma daga bisani aka mika gawarta ga iyalanta domin gudanar da jana’iza.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jigawa ya bayyana cewa waɗanda ake zargi za su fuskanci tuhume-tuhume na haɗin baki da kisan kai. Haka kuma, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP AT Abdullahi, ya bada umarnin a mika shari’ar zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ke Dutse domin gudanar da cikakken bincike.
