News
Gwamnatin Kano Ta Bankado Ma’aikata 240 Da Ke Karɓar Albashi Sau Biyu, 217 Kuma Na Amfani Da BVN Ɗaya
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana gano wasu kura-kurai a cikin tsarin biyan albashi, inda aka gano ma’aikata 240 da ke karɓar albashi sau biyu, yayin da 217 ke amfani da lambar tantance banki (BVN) ɗaya.
Mai ba Gwamna shawara na musamman kan harkokin ma’aikata, Sulaiman Sani, wanda kuma ke shugabantar Kwamitin Tsare-tsare na Jihar, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Kano a ranar Lahadi.
Ƴan Sanda Sun Damke Ango Da Abokansa Bayan Mutuwar Amarya A Jigawa
Mr. Sani, wanda ya wakilci Sakataren Gwamnatin Jihar, Umar Ibrahim, ya bayyana cewa an gano wadannan kura-kuran ne sakamakon wani binciken tantance ma’aikata ta hanyar amfani da bayanan na’ura (biometric verification), da nufin tsaftace tsarin aikin gwamnati.
A cewarsa, an gudanar da binciken ne ta hannun kwamitoci biyu — daya na matakin jiha da daya na matakin kananan hukumomi.
“Mun samu ma’aikata 240 suna karɓar albashi sau biyu, sannan kuma mun gano mutane 217 da ke amfani da BVN ɗaya,” in ji Sani.
Ya ƙara da cewa ma’aikata 1,335 ba su bayyana domin tantance su ba har fiye da watanni shida, lamarin da ya ƙara haifar da shakku game da sahihancin sunayen da ke cikin tsarin biyan albashi.
A nasa jawabin, shugaban Kwamitin Binciken Albashin Kananan Hukumomi, Umar Idi, ya ce an gano sunayen mutane 247 da ke cikin jerin albashin kananan hukumomi da na asibitocin farko da ake da shakku kansu.
“Amma daga cikin su, mutum takwas ne kawai suka bayyana domin tabbatar da matsayin aikinsu. Sauran mutum 239 an cire su daga tsarin, abin da ya haifar da ajiyar kuɗi na Naira miliyan 27.8 duk wata, wanda za a mayar wa asusun haɗin gwiwar gwamnatin jiha da na kananan hukumomi,” in ji Idi.
Mr. Sani ya jaddada cewa wannan aikin tsaftacewa ba don hukunta wani ba ne, sai dai domin tabbatar da cewa ma’aikata da ‘yan fansho na gaskiya suna karɓar hakkokinsu cikin adalci ba tare da wata cirewa ba.
Ya tunatar da cewa tun bayan hawansa kan mulki, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya fifiko wajen biyan albashi da kuma kawar da duk wani tsarin cire albashi ba bisa ka’ida ba.
“Tsaftace tsarin albashi zai ƙara gaskiya da inganci wajen gudanar da biyan albashi a jihar,” in ji Sani.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin za ta ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki domin gyara duk wasu kura-kurai da kuma dawo da martabar aikin gwamnati a Kano.
