News
Tsangayar Afirka TV3 Ta Yaye Daliban Difloma Na Farko A Shari’ar Musulunci
Tsangayar Afirka da ke ƙarƙashin tashar talabijin ta Afirka TV3, ta gudanar da bikin yaye daliban da suka kammala karatun difloma a fannin Shari’ar Musulunci ta hanyar koyarwa ta intanet, karo na farko tun kafa tsarin a shekarar 2022.
Bikin ya gudana ne a sabuwar Jami’ar Bayero, inda aka tattaro daliban da suka kammala karatunsu na shekarar 2024/2025.
Da yake jawabi a wajen bikin, Shugaban Gamayyar Rukunonin Tashoshin Afirka TV3, Dr. Habib Tijjani Taheer, ya bayyana cewa an kafa tsarin ne domin bai wa masu sha’awar karatun addinin Musulunci damar samun ilimi cikin sauƙi ko ina suke a duniya.
Ya ce, “A lokacin da muka fara tsarin, sama da dalibai dubu goma sha biyar ne suka nemi shiga, amma yanzu kusan dubu uku ne suka kammala karatun cikin nasara. Muna fatan wannan zai amfani rayuwarsu da al’ummar Musulmi baki ɗaya.”
Dr. Habib ya ƙara da cewa, “Za mu fara rijistar sababbin dalibai domin zangon karatu na biyu, tare da duba yiwuwar samar da tsarin karatun digiri nan gaba.”
A nasa ɓangaren, Farfesa Abdulkhadir Isma’il, ɗaya daga cikin malaman tsangayar, ya bayyana cewa wannan tsari zai zama wata dama ta musamman ga duk mai sha’awar neman ilimin addinin Musulunci, ba tare da tsayawa kan matsalolin tafiye-tafiye ko kuɗi ba.
Farfesan ya ce, “Ilimi shi ne makamin rayuwa, musamman a wannan lokaci da talauci ke ci gaba da kassara al’umma.”
Wasu daga cikin daliban da suka amfana da karatun sun bayyana farin cikinsu tare da nuna godiyarsu ga tashar TV3 bisa daukar nauyin karatunsu.
A ƙarshe, an karrama daliban da suka fi nuna kwarewa, inda aka ba dalibi mafi ƙwazo kyautar kujera zuwa Umara.
