News
Jami’an Hukumar NDLEA Sun Kama Ƙwayoyin Tramadol Miliyan Biyu A Kano
Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta samu nasarar cafke ƙwayoyin tramadol sama da miliyan biyu a jihar Kano.
NDLEA ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, inda ta ce an samu nasarar cafke ƙwayoyin ne bayan jami’anta sun tare wata mota ƙirar Toyota Sienna a kan hanyar Kano zuwa Jigawa. A cikin motar, an gano ƙwayoyi 200,000 na tramadol da kuma kwayoyin pregabalin guda 217,500.
Tsangayar Afirka TV3 Ta Yaye Daliban Difloma Na Farko A Shari’ar Musulunci
Bayan wannan samame, jami’an NDLEA suka bi diddigin lamarin zuwa gidan wani da ake zargi da dillancin ƙwayoyin a unguwar Mil Tara da ke Kano. A can kuma, sun gano ƙarin ƙwayoyin tramadol guda 1,584,000 da aka ajiye a cikin wata mota ƙirar Nissan.
Hakan ya sanya adadin ƙwayoyin da aka kama ya kai 2,001,500 gabaɗaya.
Wannan nasara ta biyo bayan wata irin nasarar da hukumar ta samu a makon da ya gabata, inda ta gano ɗauri 20 na hodar ibilis da aka ɓoye a cikin littattafan addini da ake shirin tura su zuwa Saudiyya. Haka kuma, a ranar Laraba 23 ga Afrilu, hukumar ta sake kama wasu ɗauri 46 na hodar ibilis mai nauyin gram 547, waɗanda aka sakaya a cikin man shafawa domin safararsu zuwa ƙasashen Gabas ta Tsakiya.
Baya ga haka, NDLEA ta ce an gano kilo 1.8 na allurar pentazocine da gram 60 na ƙwayoyin bromazepam da ake shirin aikawa zuwa Canada, a cikin wani kamfanin jigilar kayayyaki da ke Legas.
Ko da yake ana ci gaba da fuskantar matsalar safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya, hukumar NDLEA ta bayyana cewa tana samun gagarumar nasara wajen dakile ayyukan masu hannu a wannan mummunan fatauci.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
