Connect with us

News

MARTANI: Jama’ar Goronyo Sun Kare Minista Bello Goronyo Daga Zargin Mu’azu S. Rima

Published

on

IMG 20250428 WA0014

A tarihi tun bayan kafuwar Jihar Sokoto, musamman a yankin Gabas, ba a taɓa samun Minista da ya ba da cikakken goyon baya da taimako ga yankinsa irin na Barista Bello Goronyo ba.

Ayyukan alheri da cigaban da ya shimfiɗa a Goronyo sun kafa tarihin da ba za a iya gogewa ba, ko bayan shekaru aru-aru.

Advertisement

Jami’an Hukumar NDLEA Sun Kama Ƙwayoyin Tramadol Miliyan Biyu A Kano

Bincike ya nuna cewa, a duk faɗin duniya, babu wani da ya taɓa taimaka wa Mu’azu S. Rima kamar yadda Barista Bello Goronyo ya yi: ya ɗauki nauyin iyalansa, ya kula da mahaifiyarsa, ya bashi mashin hawa da kuɗi naira dubu dari biyar (₦500,000) domin ya fara sana’a, kuma ya ɗauki nauyin aikin Hajjin mahaifinsa, baya ga taimaka wa ‘yan uwansa da samun ayyuka a matakin gwamnatin tarayya.

Minista Bello Goronyo ya kawo manyan sauye-sauye a Goronyo da suka haɗa da gina tituna, samar da ruwan sha, tallafawa matasa da samar da ayyuka, gyaran masallacin Jumu’a, da kuma gyaran asibitoci. Irin wannan cigaba bai taɓa kasancewa a yankin ba a baya.

Advertisement

Sai dai wannan cigaba ya haifar da hassada daga masu ƙiyayya, inda suka nemi bata sunan Ministan ta hanyar amfani da Mu’azu S. Rima wajen ƙirƙirar ƙarya. Al’umma sun bayyana rashin yarda da waɗannan zarge-zarge, suna mai cewa wannan shiri ne na makiyan ci gaba.

Har ila yau, mahaifiyar Mu’azu S. Rima ta nuna ɓacin ranta kan ɗanta, inda ta bayyana cewa babu wani da ke taimaka mata a duniya irin Barista Bello Goronyo.

Advertisement

Muna jaddada cewa duk da irin wannan ƙoƙarin ɓata suna, Barista Bello Goronyo zai ci gaba da jajircewa wajen kawo ci gaba da taimako ga al’umma. Makiyan ci gaba ba za su hana ci gaba da yaduwa a Goronyo da gabaɗaya yankin Gabas na Jihar Sokoto ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending