News
Albashin N70,000 Ba Ya Iya Daukar Nauyin Ma’aikatan Najeriya — NAFOHEADS
Ƙungiyar Shugabannin Hukomomin Gwamnatin Tarayya a Najeriya (NAFOHEADS) ta bayyana cewa sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 da gwamnatin tarayya ta ƙaddamar, ya rasa kima kuma ba ya iya ɗaukar nauyin rayuwar ma’aikata a kasar.
Shugaban NAFOHEADS na Jihar Osun, Samuel Adekunle, ne ya bayyana haka a Osogbo ranar Laraba, yayin wani taron addu’o’in haɗin gwiwar addinai da aka gudanar a matsayin wani ɓangare na bikin makon ma’aikatan Afrika na shekarar 2025.
A wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a gefen taron, Adekunle ya ce hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa sun hana sabon albashin yin wani tasiri mai ma’ana ga rayuwar ma’aikata.
Ya ce tun bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu a kan dokar sabon mafi ƙarancin albashin a watan Yuli 2024, har zuwa lokacin da aka fara aiwatar da shi a watan Satumba, matsin tattalin arziki ya ƙara tsananta.
“Albashin Naira 70,000 da ake biya yanzu ba ya wadatar da ma’aikata. Tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya sun hana albashin yin tasiri a rayuwar mutane,” in ji shi.
Adekunle, wanda kuma shi ne Kwamishinan Gidan Tarihi da Fasaha na Ƙasa (National Gallery of Arts), ya yi kira ga gwamnati da ta sake duba sabon mafi ƙarancin albashin tare da sabunta shi bisa hakikanin yanayin tattalin arzikin kasar.
“Ya kamata a sake ƙididdige albashin bisa la’akari da halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki domin rage wa ma’aikata radadin rayuwa,” in ji shi.
NAN ta ruwaito cewa taken bikin makon ma’aikatan Afrika na bana shi ne: “Federal Civil Service and Sustainable Development in a Developing Economy”, wato: “Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da Ci Gaban Dorewa a Tattalin Arzikin da ke Ci Gaba da Haɓaka.”
