Connect with us

News

Ma’aikatan Jinya Sun Yi Watsi Da Sabon Umarnin NSIWC Kan Ƙarin Alawus

Published

on

Alawus

Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Unguwar Zoma ta Najeriya (NANNM-FHI) ta bayyana rashin amincewarta da wata sabuwar wasiƙa da Hukumar Albashi, Kuɗin Shiga da Ƙarin Albashi ta Ƙasa (NSIWC) ta fitar, wadda ke da alaƙa da sake duba tsarin alawus ga ma’aikatan lafiya.

Wasiƙar, mai lamba  SWC/S/04/S.218/III/646, wadda aka fitar ranar 27 ga Yuni, 2025, tana ɗauke da taken “Sake Duba Alawus na Likitoci/ Likitocin Hakora  Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.” Sai dai ƙungiyar NANNM-FHI ta bayyana cewa wasiƙar ta nuna babbar ƙasa da muhimmancin ma’aikatan jinya da unguwar zoma a tsarin kiwon lafiya na ƙasa.

Advertisement

Ma’aikatan Jinya Sun Yi Watsi Da Sabon Umarnin NSIWC Kan Ƙarin Alawus

A cewar shugaban ƙungiyar na ƙasa, Nurse Morakinyo-Olajide Rilwan, ƙungiyar ba ta samu wata tuntuɓa ba kafin fitar da wannan wasiƙa duk da cewa jinya na da kaso mafi rinjaye a cikin ma’aikatan lafiya a ƙasar – tsakanin 60 zuwa 70 cikin 100.

 

Advertisement

Shugaban ya bayyana cewa “Wasiƙar ta gaza shigar da ma’aikatan jinya cikin tsarin ƙarin alawus, lamarin da ya nuna bambanci da raina ƙoƙarin da muke yi wajen kula da lafiyar jama’Alawusda cewa an bar wasu muhimman alawus da suka shafi ma’aikatan jinya a gefe, kamar Alawus na aiki da dare, Alawus na kayan aiki (uniform) ,Alawus na ƙwarewa (specialist), da kuma na kiran gaggawa, Alawus na riƙewa (retention).

Nurse Rilwan ya ce ma’aikatan jinya na fuskantar kalubale na musamman da ke buƙatar su sauya kayan aiki fiye da sau ɗaya a rana, don haka ya zama dole a ɗauki batun kayan aiki da muhimmanci.

Advertisement

Ya bayyana cewa ƙungiyar a shirye take ta shiga tattaunawa da gwamnati don warware matsalar cikin lumana.

Sai dai ya jaddada cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, za su iya ɗaukar matakin yajin aiki don kare muradunsu.

Advertisement

“Ba ma son ɗaukar matakin yajin aiki, amma idan aka cigaba da yin biris da mu, ba za mu yi shiru ba.” in ji shi.

 

Advertisement

 

SOLACEBASE

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending