Connect with us

News

Jihar Kano Ta Fi Kowace Jiha Yawan Sabbin Masu Rijistar NIN A Bana — NIMC

Published

on

images (5)

Jihar Kano ce ta fi sauran jihohin Najeriya yawan sabbin masu rijistar Lambar Shaidar Dan Kasa ta Najeriya (NIN) tsakanin watan Janairu zuwa Yuni na shekarar 2025.

Alkaluman da Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC) ta fitar, kuma jaridar NIGERIAN TRACKER ta ruwaito cewa  Kano ta samu fiye da mutum miliyan 1.01 da suka yi sabuwar rijista a cikin watanni shida na farkon shekarar.

Advertisement

Wannan adadi ya ba Kano tazarar nisa da jihar Legas, wadda ke a matsayi na biyu da 412,220, sai Kaduna a matsayi na uku da 309,620.

Jihohin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma su ma sun nuna gagarumar nasara a wannan fanni. Adamawa ta samu 217,650, Borno 209,500, Babban Birnin Tarayya Abuja 209,240, yayin da Kebbi ta samu 192,050.

Advertisement

A Kudancin Najeriya, Ogun ce ta fi kowa da 187,490, sai Oyo da 183,600, Akwa Ibom 176,850, da kuma Rivers da 141,020. Delta ta samu 123,910.

Sai dai wasu jihohi da ke kasa a jerin sun hada da Zamfara da 50,800, Bayelsa 46,470, da Gombe 42,340. Cross River (27,210), Ekiti (26,640) da Kogi (26,040) su ne suka fi ƙarancin rijista, lamarin da ya haifar da damuwa game da yadda tsarin ke tafiya a wasu yankuna.

Advertisement

Baya ga haka, ’yan Najeriya mazauna kasashen waje sun yi rijistar 49,950 na sabbin NIN daga watan Janairu zuwa Yuni na shekarar.

A cewar NIMC, ƙaruwa a yawan rijistar na da nasaba da yawaitar cibiyoyin rajista, sabbin motocin rajista da ke kai tsaye zuwa ƙauyuka da birane, da kuma wayar da kan jama’a da gwamnati ke yi a fadin ƙasar.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa mallakar NIN na da matuƙar muhimmanci wajen samun ayyukan gwamnati, takardar fasfo, buɗe asusun banki, da rajistar layin waya.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending