Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Bijire Wa Muradin Amurka

Published

on

tinubu 1

Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya bayyana cewa Najeriya ba za ta amince da matsin lamba da Amurka ke yi na karbar ‘yan Venezuela da Amurka ta kama a cikin a kasarta ba.

Tuggar ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Najeriya a ranar Jumma’a, inda ya ce shugaban Amurka, Donald Trump, yana kokarin tilasta wa kasashen Afirka karbar ‘yan Venezuela da aka kama da laifin zama a Amurka ba bisa ka’ida ba.

Jihar Kano Ta Fi Kowace Jiha Yawan Sabbin Masu Rijistar NIN A Bana — NIMC

Ministan ya ce kimanin mutane 300 ciki har da wasu masu laifi da aka fito da su daga gidajen yari shugaban na Amurka ke son Najeriya ta karbe su, yana mai cewa baya ga Najeriyar akwai wasu karin kasashen Afirka da shugaba Trump ke bukatar su ma su karbi bakin hauren na Venezuela.

Babban jami’in diflomasiyyar Najeriyar ya ce kasarsa na fuskantar nata matsaloli masu nauyi, don haka ba za ta iya daukar nauyin wani karin kalubale ba, yana mai fargabar idna har Najeriya ta karbi wannan bukata ta bude kofar bai wa murkan damar jibge mata bakin haure a kasarta.

 

 

Advertisement

DW

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending