Connect with us

News

‎Yaro Dan Shekara Uku Ya Rasu Bayan Faɗawa Cikin Budaddiyar Masai

Published

on

Budaddiyar Masai

‎Wani yaro ƙarami mai suna Chibuike Uba, ɗan shekara uku, ya rasa ransa bayan da ya faɗa cikin wata budaddiyar masai a unguwar Babarinsa da ke Ibeju-Lekki, Jihar Legas.

‎Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, yayin da mahaifiyar yaron, Utoro, ta kai wa yayarta ziyara daga Epe inda take zaune.

Advertisement

Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kama Mata Biyu Da Ake Zargi da Satar Atamfofi

‎Binciken da DAILY POST ta gudanar ya gano cewa, yayin da mahaifiyar ke tattara kayanta domin komawa gida, ɗanta ya bi yayarta waje da ta fita amsa waya. Bayan ta dawo, ba a sake ganin yaron ba, lamarin da ya tayar musu da hankali.

‎A yayin bincike, mahaifiyar ta hango takalmin ɗanta a bakin wata Budaddiyar Masai da ke makwabtaka da gidan yayarta

Advertisement

‎Utoro ta bayyana wa wakilin DAILY POST cikin kunci cewa ,“Da na ga takalmin ɗana a bakin Budaddiyar Masai , sai na fahimci abin da ya faru. Na fara ihun neman taimako, muka kwashi yaron muka garzaya da shi asibiti.”

‎An fara zuwa da Yaron wani asibiti mai zaman kansa a yankin Sapati, daga nan aka tura su zuwa Asibitin Gwamnati da ke Akodo. Duk da an saka shi a kan na’urar taimakon numfashi, daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.

Advertisement

‎Utoro ta zargi sakaci daga bangaren mai gidan, inda ta bayyana cewa yayarta ta sha fadakar da shi kan hadarin da budaddiyar masar najasa ke haifarwa, amma ya gaza rufe ta.

‎Lamarin ya haifar da damuwa a tsakanin mazauna yankin, inda suke kira ga gwamnati da ta tilasta wa masu gidaje su rufe irin wadannan gurare domin kare rayukan mutane, musamman yara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending