News
Gwamnati Ta Shirya Dakile Amfani Da Itace wajen Girki A Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta bayyana shirin ta na daukar matakan hana amfani da itace da rishon gargajiya wajen girki, a wani bangare na kokarinta na kare lafiyar mata da bunkasa tattalin arzikin gida.
Ministar Kula da Harkokin Mata, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta bayyana hakan a wata ganawa da aka yi a Abuja ranar Laraba tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki a fannin makamashi. Ta ce sama da mata 800,000 ne ke mutuwa a kowacce shekara sakamakon shakar hayakin da ke fita daga itacen girki, lamarin da ke barazana ga lafiyar mata da kuma hana su ci gaba a harkokin tattalin arziki.
Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Aikin Titin Northern Bypass Daga Danzaki Zuwa Dawanau
Imaan ta bayyana cewa gwamnati za ta maye gurbin amfani da itace da na’urorin girki na zamani da ke amfani da hasken rana, musamman a karkara, domin inganta harkokin noma da rage radadin wahalar da mata ke fuskanta wajen nemo itace.
Shugaban Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Yankunan Karkara (REA), Injiniya Abba Abubakar-Aliyu, ya bayyana cewa gwamnati ta ware dala miliyan 550 domin aikin samar da wuta ga mutane miliyan takwas da kuma tallafawa sana’o’in hannu 35,000. Sana’o’in hannu 12,000 daga cikin su kuwa, mata ne ke da su.
Ya kara da cewa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ware dala miliyan 750 domin bunkasa samar da wuta a fadin kasar, inda dala miliyan 410 za a yi amfani da su wajen wutar lantarki a karkara, da kuma dala miliyan 240 wajen samar da na’urorin da ke amfani da hasken rana.
Shugaban Hukumar NASENI, Khalil Halilu, ya jaddada cewa rashin samun makamashi na zamani matsala ce da ke hana mata samun ci gaba da kuma cutar da lafiyarsu, inda ya yabawa wannan sabon tsarin gwamnati a matsayin mai matukar muhimmanci.
Wannan sabon shirin na gwamnati ana sa ran zai canza rayuwar miliyoyin mata a fadin Najeriya, tare da inganta lafiyarsu da inganta tattalin arzikin kasa baki daya.
