News
Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Aikin Titin Northern Bypass Daga Danzaki Zuwa Dawanau
Gwamnatin Tarayya ta amince da aiwatar da aikin gina titin Northern Bypass mai tsawon kilomita 74, wanda zai hada Garin Danzaki da Dawanau, a karamar hukumar Dawakin Tofa. Wannan mataki ya samu karbuwa bayan tattaunawar da aka gudanar a tsakanin hukumomi da al’ummomin yankin.
Al’ummar Danzaki, a baya, sun nuna damuwa game da tasirin aikin kan gidajensu, gonakinsu, makarantu da makabartu, inda suka zargi cewa za a kwace musu wasu daga cikin wadannan muhimman wurare. Duk da haka, Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa za a bi dukkan ka’idojin da suka dace wajen gudanar da aikin, tare da baiwa wadanda za a shafa diyya bisa ga dama da hakkin su.
Kotu ta Daure Wani Mutum Saboda Sare Bishiya Ba Bisa Ka’ida Ba A Kano
Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka ta Kasa, wanda ya jagoranci tawagar da ta ziyarci Kano domin duba shirin aikin, ya bayyana cewa an cimma matsaya cewa aikin zai ci gaba daga wuraren da aka tsara daga farko. Ya kuma jaddada cewa, Ma’aikatar Ayyuka ta Kasa za ta biya diyya ga masu gonaki, store da filayen da za a taba sakamakon aikin titin.
AREWA RADIO ta ruwaito cewa dukkan bangarorin sun amince da wannan yarjejeniya, inda kowanne bangare ya rattaba hannu kan cewa zai bayar da cikakken hadin kai ga ma’aikatan aikin da kuma tabbatar da zaman lafiya yayin aiwatar da aikin. Wannan yarjejeniya ta zama mataki mai kyau wajen tabbatar da cigaba da ci gaban yankin tare da kare hakkin al’umma.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
