News
Kotu ta Daure Wani Mutum Saboda Sare Bishiya Ba Bisa Ka’ida Ba A Kano
A cikin wani lamari mai alaka da kiyaye muhalli, wata Kotun Majistare a Rijiyar Zaki, Kano, ta yanke wa Alhaji Inuwa Ayuba hukuncin daurin watanni biyu a gidan yari ko biyan tara sakamakon laifin sare bishiyoyi bakwai a kauyen Sarauniya, dake karamar hukumar Dawakin Tofa.
Lauyar masu gabatar da kara daga ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi, Barista Bahijja H. Aliyu, ta bayyana cewa an samu labarin cewa an sare itatuwan Neem ba bisa ka’ida ba a kauyen Sarauniya, wanda ya saba da dokokin kiyaye muhalli na jihar Kano. Wannan ya sa aka yi gaggawar cafke wanda ake tuhuma tare da tattara hujjoji na shari’a kafin a gurfanar da shi gaban kotu.
Bayan duba shaidun da aka gabatar, kotun ta yanke hukunci na daurin watanni biyu a gidan yari ko kuma biyan tara, sannan kuma ta umurci wanda ake tuhuma da dasa itatuwan Neem guda 14 a matsayin hukuncin laifin da ya aikata.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahiru M. Hashim, ya nuna godiya ga kokarin jami’an sa ido na ma’aikatar da bangaren shari’a bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen kare muhalli.
Ma’aikatar muhalli ta kuma yi kira ga mazauna yankin da su bi ka’idojin muhalli da suka hana gurɓata muhalli, tare da kai rahoton duk wani abu da zai iya lalata muhalli ga hukumomin da suka dace. Wannan ya nuna kokarin ma’aikatar a yaki da gurbatar muhalli, inda suka samar da dokoki da ke bai wa Dazuka kariya da kuma hana sare itatuwa ba bisa ka’ida ba.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News6 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
