Connect with us

News

ICPC Ta Yi Amai Ta Lashe Kan Sanarwar Binciken Kuɗaɗen Bashin Karatu

Published

on

images

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (ICPC) ta ce ta yi kuskure a sanarwar da ta fitar dangane da kuɗaɗen bashin karatu da aka ware wa ɗalibai ta hannun hukumar NELFUND.

Tun da farko, ICPC ta fitar da sanarwa a ranar Alhamis, inda ta nuna cewa daga cikin naira biliyan 100 da aka ware domin bayar da bashin karatu, ana zargin naira biliyan 71 sun ɓace ba tare da takamaiman bayani ba.

Advertisement

‎Saudiyya Ta Sanya Sabbin Matakai Da Tara Masu Tsauri Kan Ƙoƙarin Hajji Ba Tare Da Izini Ba

Sai dai shugaban hukumar, Barista Musa Adamu Aliyu, ya bayyana a wata tattaunawa da ya yi da BBC cewa an samu kuskure wajen fassara ko fitar da bayanan binciken.

“Binciken da muke yi ba ya kan hukumar NELFUND kai tsaye, sai dai akan wasu jami’o’i da ake zargin ba sa bai wa ɗalibai kuɗaɗen da aka tura musu,” in ji shi.

Advertisement

Ya ce tsarin da NELFUND ke amfani da shi shi ne tura kuɗin karatu kai tsaye zuwa asusun jami’o’i, sannan kuma a tura kuɗin kashewa zuwa asusun ɗalibai kai tsaye.

Barista Aliyu ya ce korafe-korafen da suka taso sun shafi yadda wasu jami’o’i ke ƙin amincewa da cewa an tura musu kuɗaɗen karatun, duk da cewa ɗalibai sun tabbatar sun karɓi kuɗin kashewa daga NELFUND.

Advertisement

Haka kuma, wasu ɗaliban na zargin jami’o’in da cajin su kuɗaɗe da suka wuce yadda aka kayyade a cikin kuɗin karatun.

Dangane da batun batan kuɗi kuwa, shugaban na ICPC ya bayyana cewa “ba gaskiya ba ne cewa an sace ko an ɓata wani kuɗi daga cikin na bashin karatu. Kuskure ne kawai aka samu a sanarwar da muka fitar tun da farko.”

Advertisement

Ya ƙara da cewa yanzu sun fito fili suka bayyana gaskiyar abin da ke faruwa domin guje wa ƙarin rudani.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending