Connect with us

News

JAMB Ta Ce Ba Ta Da Alaka da Shafin Da Ke Karɓar Kuɗi Daga Hannun Ɗaliban Da Suka Rasa UTME

Published

on

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a (JAMB) ta nesanta kanta da wani shafi da ke karɓar kuɗi daga hannun ɗaliban da suka rasa jarabawar UTME ta 2025.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Laraba, ta ce wani shafi da ake kira ‘Copyrightwriter Personal J Rescheduling Flw’ da kuma asusun banki na Sterling mai lamba 8520641017 ana amfani da su ne wajen yaudarar ɗalibai.

Advertisement

ICPC Ta Yi Amai Ta Lashe Kan Sanarwar Binciken Kuɗaɗen Bashin Karatu

Mai magana da yawun hukumar, Dr Fabian Benjamin, ya ce an ƙirƙiri shafin ne da nufin karɓar kuɗi daga hannun waɗanda suka gaza rubuta jarabawar, da sunan za a sake musu lokaci.

“Wasu marasa gaskiya na karɓar kuɗi har Naira 15,700 daga ɗalibai da zargin za su taimaka musu su sake jarabawa. Wannan ba gaskiya ba ne, zamba ce tsagwaronta,” in ji shi.

Advertisement

JAMB ta bayyana cewa ba ta da hannu a wannan aiki kuma ba ta da alaƙa da masu gudanar da shi. Haka kuma ta bukaci Sterling Bank da ta dauki matakin toshe asusun da ke karɓar kuɗin.

Ta ce tana aiki da jami’an tsaro domin kamo waɗanda ke da hannu a lamarin.

Advertisement

Dr Benjamin ya ƙara da cewa JAMB ba ta sake wa ɗalibi lokaci na jarabawa idan gazawarsa ta faru ne sakamakon kuskurensa ko wani dalili da bai shafi hukumar ba.

Sai dai in an samu matsala wajen tantance shi ta hanyar biometric, kuma an tabbatar da sahihancin matsalar, JAMB za ta ba shi damar sake rubuta jarabawar kyauta.

Advertisement

“Babu wani kuɗi da JAMB ke karɓa bayan an kammala rajista. Don haka muna kira ga ɗalibai da su guji fadawa tarkon ’yan damfara,” in ji shi.

Ya kuma shawarci jama’a da su rika kai rahoton duk wata alamar damfara da suka fuskanta ga hukuma cikin gaggawa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending