Connect with us

News

NDLEA Ta Kwace Kwayoyi Na Sama Da Biliyan 6.5, Ta Kama Ƴan Birtaniya 

Published

on

WhatsApp Image 2025 05 25 at 10.33.52 750x430

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta ce ta kwace miyagun kwayoyi da darajarsu ta kai Naira biliyan 6.524 a wasu tashoshin jiragen ruwa da ke Fatakwal da Legas.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi daga Abuja, ya ce an gano kwayoyin ne sakamakon wani bincike na musamman da aka gudanar, bayan samun bayanan sirri kan sabbin hanyoyin da masu safarar kwayoyi ke bi don shigo da su cikin ƙasa.

Advertisement

JAMB Ta Saki Sakamakon Ɗaliban Da Suka Sake Rubuta Jarrabawa

Babafemi ya ce kwayoyin da aka kwace sun haɗa da nau’o’in Tramadol, Tapentadol, Carisoprodol, da kuma kwalaye 332,000 na maganin tari mai ɗauke da sinadarin Codeine.

Ya ce an kama kayan ne a cikin kwantena biyu da aka bude a tashar jirgin ruwa ta Onne a ranakun 19 da 20 ga watan Mayu. Haka kuma, a ranar 22 ga watan Mayu, jami’an NDLEA tare da hadin gwiwar Kwastam da sauran jami’an tsaro sun gano kwalaye 170,000 na maganin tari mai haɗari a tashar Apapa da ke Legas.

Advertisement

A wani samame daban, NDLEA ta ce ta cafke wasu mutane huɗu da suka haɗa da ‘yan Birtaniya biyu da kuma ‘yan Najeriya biyu da ke ƙoƙarin shigo da tabar wiwi nau’in Loud mai nauyin kilogiram 51.10 ta filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas.

Shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya yabawa jami’an hukumar bisa jajircewa da kuma kokarinsu na hana safarar kwayoyi da kuma rage amfani da su a cikin al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending