News
Wani Matashi Ya Rasa Ransa Saboda Ya Ziyarci Budurwarsa A Kano
Wani matashi ya rasa ransa a kauyen Tarandai da ke karamar hukumar Takai a jihar Kano, bayan da wasu matasa suka kai masa farmaki saboda ya je zance wajen budurwarsa.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu, da misalin karfe 7:45 na yamma, a cewar rahotanni daga yankin.
NDLEA Ta Kwace Kwayoyi Na Sama Da Biliyan 6.5, Ta Kama Ƴan Birtaniya
Majiyoyi sun ce rikici ya barke tsakanin matasan kauyukan Faruruwa da Tarandai a ranar kasuwarsu, wanda hakan ya kai ga kashe matashin mai suna Sani Yunusa, mai shekaru 28, ɗan asalin kauyen Toho Diribo.
Wani mazaunin yankin ya ce, “An kai masa hari da adduna da sanduna yayin da yake dawowa daga wajen budurwarsa a kauyen Tarandai.”
Rahotanni sun kuma ce lamarin ya haddasa konewar shaguna a kasuwar wucin gadi da ke tsakanin kauyukan biyu.
Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa ta tura jami’anta domin dakile ci gaba da rikicin, tare da tabbatar da zaman lafiya a yankin.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
