Connect with us

News

Mutane 1,450 Na Jiran Shari’a Kan Zargin Ta’addanci A Najeriya — JIC

Published

on

Cibiyar Bincike ta Haɗin Gwiwa (JIC) ta ce mutum 1,450 da ake zargi da ta’addanci na jiran a gurfanar da su a gaban kotu a sassa daban-daban na Najeriya.

Mukaddashin kwamandan JIC, Kanal AU Ahmed, wanda Olugbenga Adeniyi ya wakilta ne ya bayyana hakan a Maiduguri yayin da yake bayani ga manema labarai kan ayyukan cibiyar.

Advertisement

Kano Ta Zama Cibiyar Bincike Da Maganin Cututtuka Na Zamani — Farfesa Salihu

Ya ce adadin na cikin mutum 1,877 da ake zargi da hannu a ta’addanci da cibiyar ke bincike kansu.

“Mun raba su gida uku: na farko — wadanda za a yanke wa hukunci; na biyu — wadanda za a sabunta musu tunani; da na uku — wadanda za a sake mayar da su cikin al’umma,” in ji shi.

Advertisement

Ya ce wadanda za su fuskanci shari’a an kai su sansanin Giwa da ke Kainji, yayin da waɗanda aka tantance za a sake su aka mika su ga gwamnatin jihar Borno.

Kanal Ahmed ya ce babban kalubale da suke fuskanta shi ne rashin shaidu.

Advertisement

“Muna shan wahala wajen samun shaidu da za su goyi bayan bincikenmu. Wasu wuraren ba a iya zuwa saboda hadari, sannan mutane da dama na tsoron bayar da shaida,” in ji shi.

Ya kuma nuna cewa akwai jinkiri wajen yanke hukunci, duk da an kammala bincike kan wasu daga cikin wadanda ake tsare da su.

Advertisement

“Wannan jinkiri na janyo tsaiko a aikace-aikacenmu, musamman wajen cika manufofin da muka sa gaba,” in ji shi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa akwai kiraye-kiraye da dama daga kungiyoyi da masana na a kafa kotuna na musamman da za su rika hanzarta yanke hukunci kan laifukan ta’addanci.

Advertisement

 

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending