Connect with us

News

Rikicin Rano: Kungiyar One Kano Agenda Ta Nemi Jama’a su Kwantar Da Hankali

Published

on

IMG 20250528 WA0030

Kungiyar One Kano Agenda ta bayyana damuwa kan rikicin da ya barke a karamar hukumar Rano da ke Jihar Kano, inda ta bukaci jama’a da su kwantar da hankali tare da bin doka da oda domin a samu zaman lafiya mai dorewa.

A cikin wata sanarwa da Sakataren kungiyar, Barrister Mukhtar Musa, ya fitar, kungiyar ta ce dole ne kowa da kowa ya taka rawa wajen ganin an dakile rikicin kafin ya kazanta.

Advertisement

Mutane 1,450 Na Jiran Shari’a Kan Zargin Ta’addanci A Najeriya — JIC

“’Yan sanda su nuna kwarewa da gaskiya a aikinsu. Kada su nuna bangaranci ko su yi shiru a lokacin da ake bukatar su tsoma baki. Jama’ar Rano na bukatar tsaro mai adalci, ba tsangwama ba,” in ji sanarwar.

Kungiyar ta kuma bukaci matasa da su guji tada zaune tsaye ko daukar fansa, domin hakan ba zai haifar da da mai ido ba.

Advertisement

Kiran da One Kano Agenda ke yi:

Ga ‘Yan Sanda: Ku kare kowa da kowa ba tare da nuna bambanci ba. Ku yi aiki da gaskiya da kwarewa.

Advertisement

Ga Jama’ar Rano: Ku kwantar da hankali. Kada ku ɗauki doka a hannu, ku rika kai rahoto ga hukumomi.

Ga Gwamnatin Kano: A gaggauta shawo kan lamarin, tare da kafa kwamiti da zai hada dukkan bangarori domin sasanci.

Advertisement

Ga Shugabannin Addini da Na Gargajiya: Ku rika jawo hankalin mutane kan muhimmancin zaman lafiya da hakuri.

“Zaman Lafiyar Rano Zaman Lafiyar Kano ne”

Advertisement

Kungiyar One Kano Agenda ta jaddada cewa rikicin da ya shafi Rano yana iya shafar sauran sassan jihar, saboda haka akwai bukatar hadin kai domin hana abin kazanta.

“One Kano ba wai suna ba ne kawai, wani kudiri ne na tabbatar da zaman lafiya da adalci a tsakaninmu gaba daya,” in ji kungiyar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending