Connect with us

News

An Kama Sojoji 18 Da ‘Yan Sanda 15 Da Ake Zargi da Siyar Da Makamai Ga ‘Yan Ta’adda

Published

on

yan bindiga sun sace mutane

Rundunar sojojin Najeriya da ke karkashin aikin musamman na Operation Hadin Kai ta kama jami’an tsaro 33 – ciki har da sojoji 18 da ‘yan sanda 15 – bisa zargin hannu cikin siyar da makamai da harsasai ga ‘yan ta’adda da wasu bata-gari.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Manjo Ademola Owolana, a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, dangane da nasarorin da rundunar ta samu daga shekarar 2024 zuwa farkon 2025.

Advertisement

Rikicin Rano: Kungiyar One Kano Agenda Ta Nemi Jama’a su Kwantar Da Hankali

Manjo Owolana ya bayyana cewa an kama jami’an ne sakamakon wani shiri da ake gudanarwa mai suna Operation Snowball, wanda aka kaddamar a watan Agustan 2024 domin gano bakin zaren sace-sacen makamai da harsasai a cikin rundunonin tsaro da kuma hana yaduwar su zuwa hannun masu aikata laifuka.

“Binciken ya shafi jihohi 11 tare da babban birnin tarayya, kuma an kama jami’an da ake zargi a sassa daban-daban na kasar nan ciki har da Bauchi, Benuwe, Borno, Ebonyi, Enugu, Legas, Filato, Kaduna, Ribas, Taraba da Abuja,” in ji Manjo Owolana.

Advertisement

Wannan mataki na daga cikin kokarin rundunar hadin gwiwa wajen tabbatar da tsaro da kawar da barazanar da ke gurgunta zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas da kasa baki daya.

Rundunar ta tabbatar da cewa za a gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a gaban kuliya domin girbar abin da suka shuka, tare da ba da tabbacin cewa hukumomin tsaro ba za su yarda da cin amanar kasa daga cikin nata ba.

Advertisement

 

 

Advertisement

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending