News
Abin Da Ya Sa Muka Fi Mayar Da Hankali Kan Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi – Ribaɗu
Mai baiwa shugaban ƙasa shawara na musamman kan tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu, ya bayyana cewa dalilin da ya sa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta fifita yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi shi ne domin tasirin muggan ƙwayoyi wajen haddasa aikata laifuka da rikice-rikice a ƙasar nan.
Ribaɗu ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a Abuja, inda ya jaddada cewa akwai haɗin kai da fahimtar juna tsakanin ofishinsa da Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), domin tabbatar da nasarar wannan fafutuka.
Ba Na Taƙaddama Da Yara — Amaechi Ya Mayar Da Martani Kan Wike
Ya ce, “Yawancin matsalolin tsaro da muke fuskanta a Najeriya, kama daga garkuwa da mutane, fashi da makami, da ta’addanci – duk suna da alaƙa da shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi. Wannan ya sa muka ɗauki wannan yaki da matuƙar muhimmanci.”
Ribaɗu ya yaba da namijin kokarin da shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ke yi wajen jagorantar yaƙi da miyagun ƙwayoyi a fadin ƙasar, inda ya ce hadin gwiwa da hukumomin tsaro da na shari’a na kara tabbatar da nasara.
A cewarsa, gwamnatin tarayya na da cikakken kuduri wajen kawo ƙarshen wannan barazana, domin samar da tsaro da kwanciyar hankali ga ‘yan ƙasa.
