Connect with us

News

Turmutsitsi ya yi sanadiyyar rayukan mutun 11 a Indiya

Published

on

Mutanen sun mutu ne a yayin da suke bukin murnar nasarar da kungiyar wasan kurket ta samu a birnin Bengaluru.

Magoya bayan ‘yan wasan kurket cikin farin ciki sun yi dafifi don taryar jaruman su, da ake kira Royal Challengers Bengaluru, bayan sun doke Punjab Kings a wasan karshe na gasar kurket na Premier ta Indiya a daren Talata.

Advertisement

Abin Da Ya Sa Muka Fi Mayar Da Hankali Kan Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi – Ribaɗu

Amma farin cikin na dimbin jama’a ya rikide zuwa bakin ciki da jimami, wanda da Firaminista Narendra Modi ya kira shi da babban tashin hankali. Babban ministan jihar Karnataka Siddaramaiah ya ce, mutane 11 da suka mutu matasa ne, daura da wasu 47 da suka jikkata.

Ya kara da cewa, babu wanda ya yi tsammanin fitowar jama’a irin wannan, kasancewar filin wasan yana da karfin daukar mutane dubu 35 kacal, amma wajen mutane dubu 200 zuwa 300 ne suka zo.

Advertisement

 

DW

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending