News
Yaɗa Bayanan Ƙarya Da Jita-Jita Sun Rura Wuta A Lokacin Yakin Basasa — Obasanjo
Tsohon Shugaban Ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa yaɗa bayanan ƙarya da jita-jita marasa tushe sun taka gagarumar rawa wajen ƙara hargitsi da tayar da jijiyoyin wuya a lokacin Yakin Basasa da ya auku a Najeriya tsakanin 1967 zuwa 1970.
Obasanjo ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin taron bita na shekara-shekara karo na shida da Kwalejin Yaƙi ta Sojojin Nijeriya (Army War College Nigeria – AWCN) ta shirya a birnin tarayya Abuja.
Taken taron mai taken: “Rawar da Disinformation ta Taka a Yakin Basasa na Najeriya”, ya jaddada mahimmancin fahimtar barazanar yaɗa ƙarya a fagen yaƙi da zaman lafiya, musamman a wannan zamani da duniya ke fuskantar sabon salo na yaƙi na zamani (asymmetric warfare).
A cewar tsohon shugaban, “Ƙananan runduna da ba su da ƙarfin soja na amfani da dabarun yaɗa ƙarya da farfaganda don ɓata suna da rage ƙarfin manyan runduna. Wannan salon yaƙi ya taimaka ƙwarai wajen tunzura zukata da rura wutar rikici.”
Ya ce hakan ya kara dagula lamarin Yakin Basasa, inda ya bayyana cewa makiya zaman lafiya da ‘yan ta’adda na amfani da irin wannan dabarar a yau, musamman a Arewa maso Gabas da wasu sassan ƙasar nan.
Obasanjo ya bukaci a ɗauki darasi daga tarihi, yana mai cewa akwai buƙatar Najeriya ta zurfafa bincike da nazarin tarihin sojoji don fahimtar yadda za a guji sake fadawa irin wannan hali.
A nasa bangaren, bako na musamman, Farfesa Christopher Ogbogbo, wanda shi ne Shugaban Jami’ar Admiralty, ya bayyana yadda kafafen yaɗa labarai da farfaganda suka kasance manyan kayan aiki wajen rinjayar ra’ayin jama’a da sauya akalar manufofin gwamnati a lokacin yakin.
Ya ce: “Dole ne mu fahimci rawar da labarai da aka sarrafa suka taka, domin hakan yana da tasiri mai zurfi ga makomar ƙasa da zaman lafiyarta.”
