News
Dole Ne a Karfafawa Likitoci Gwiwa Domin Su Zauna a Gidao Nijeriya – Obasanjo
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce akwai buƙatar gwamnati da masu ruwa da tsaki su samar da kyakkyawan yanayin aiki da ƙarin ƙwarin gwiwa ga likitoci da nas da aka horas a cikin gida, domin kada su cigaba da barin ƙasar zuwa ƙasashen ƙetare.
Obasanjo ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da yake buɗe asibitin Yariman Bakura da aka gyara a jihar Zamfara, ƙarƙashin gayyatar Gwamna Dauda Lawal.
Sojoji Sun Cafke Ƴan Bindiga, Sun Ƙwato Makamai A Kaduna Da Filato
Tsohon shugaban ya nuna damuwarsa kan yadda matasa da dama ke barin Najeriya zuwa ƙasashen Turai, Amurka, Asiya da sauran yankuna domin samun rayuwa mafi inganci, lamarin da ake kira da “Japa”.
A cewarsa, wannan matsalar tana cigaba da haddasa giɓi a fannin lafiya, musamman ganin yadda ƙwararrun likitoci ke barin aiki a cikin gida.
