News
Ce-Ce-Ku-Ce Ya Barke Akan Shirin Wike Na Ginin Sabuwar Hedikwatar INEC
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana aniyarsa ta fara aikin gina sabuwar hedikwatar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), al’amarin da ya haifar da muhawara mai zafi a kafafen sada zumunta, musamman ganin cewa hukumar INEC na zaman mai cin gashin kanta a tsarin mulkin ƙasar.
Wike ya bayyana haka ne a ranar Talata, ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na dandalin X (tsohon Twitter), inda ya ce Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ƙaddamar da tashar mota ta Mabushi da kuma aikin sabuwar hedikwatar INEC.
Dole Ne a Karfafawa Likitoci Gwiwa Domin Su Zauna a Gidao Nijeriya – Obasanjo
A cewarsa “A yau za mu ƙaddamar da tashar mota ta Mabushi. Za kuma mu ƙaddamar da aikin sabuwar hedikwatar INEC…”
Sai dai daga bayan sanarwar, jama’a da dama sun fara nuna shakku da damuwa kan wannan yunkuri, musamman ma ganin cewa ana zargin akwai wata manufa ta ɓoye da ka iya shafar sahihancin harkokin zaɓe a nan gaba.
Wani mai amfani da X mai suna @Omoluabi1sq ya ce:“Me ya sa Ministan FCT zai gina hedikwatar INEC? INEC ba hukumar da ke da ‘yancin kanta ba ce? Idan har tana bukatar sabon gini, ba ya kamata a sanya shi a cikin kasafin kuɗinta ba? Ko yanzu INEC ƙarƙashin ma’aikatar FCT take?”
Ya ƙara da cewa: “Wike ya rage da shekaru biyu a ofis, kuma dole ne ya fuskanci tambayoyi daga al’umma kan abubuwan da ya yi.”
Shi ma wani mai amfani da X mai suna @Joshuaezs ya bayyana ra’ayinsa da cewa“Wannan wani abu ne da ya kamata a tashi tsaye a kai. A tsarin dimokuraɗiyya, INEC dole ta kasance mai cikakken ‘yanci daga kowane ɓangare na gwamnati.”
Wani kuma, @Ezeani_malik1, ya wallafa cewa:“Wike yana shirin yi wa tsarin zaɓe kutse karo na biyu. Wannan karon ba za mu lamunta ba.”
Wasu na ganin wannan mataki wata alama ce ta haɗin gwiwar siyasa tsakanin Wike da Shugaba Tinubu, musamman duba da yadda ake hasashen cewa Tinubu na shirin tsayawa takarar tazarce a zaɓen 2027, yayin da Wike ke ci gaba da taka rawa a jam’iyyar adawa ta PDP.
Ko yaya al’amarin yake, dai, ce-ce-ku-ce kan wannan mataki na Ministan FCT na ci gaba da ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya, musamman masu kishin gaskiya da adalci a harkokin zaɓe da dimokuraɗiyya.
