News
Tsohon Ministan Ilimi Farfesa Jibril Aminu, Ya Rasu Yana Da Shekaru 85 A Duniya.
Babban masani a fannin likitanci kuma tsohon Ministan Ilimi da Fetur, Farfesa Jibril Muhammad Aminu, ya rasu yana da shekaru 85 a duniya.
Farfesa Aminu ya rasu ne a ranar Alhamis a birnin Abuja, bayan fama da jinya da ya ɗauki lokaci yana yi. Marigayin ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ’yan siyasa da masana a fannin ilimi da kiwon lafiya a Najeriya.
A lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya riƙe muƙamin Jakadan Najeriya a ƙasar Amurka tsakanin shekarar 1999 zuwa 2003. Daga nan kuma aka zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar mazabar Adamawa ta Tsakiya daga 2003 zuwa 2011.
Farfesa Aminu ya bar tarihin nagarta da kishin ƙasa, inda ya taka muhimmiyar rawa a harkokin ilimi, diflomasiyya da kuma majalisar dokoki.
Advertisements
