Sports
Tsohon Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti Zai Yi Zaman Gidan Kaso Na Shekara Guda
Wata kotu a Sifaniya ta yanke wa tsohon Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti hukuncin zaman gidan yari na shekara guda kan laifin haraji.
Ancelotti wanda shi ne kocin tawagar Brazil a yanzu ya aikata laifukan ne yayin da yake horar da Real Madrid a Sifaniya.
Fiye Da Mutane 2,000 ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Watanni Shida A Najeriya —NHRC
An zargi Ancelotti ne kan zambatar baitul malin ƙasar a shekarun 2014 da 2015 lokacin yana manajan Real Madrid a karon farko.
Yayin shari’arsa, kocin ɗan asalin Italiya ya faɗa wa kotu cewa ba shi da niyyar zambatar gwamnati ta hanyar ɓoye kuɗaɗen da yake samu masu alaƙa da haƙƙin amfani da hotuna, kuma duk abin da ya yi, wanda ƙungiyarsa ta saka shi ne.
A watan Afrilu, Ancelotti ya ƙi amsa laifinsa yayin da masu shigar da ƙara suka nemi kotu ta ba yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru huɗu da wata tara.
A yanzu kotu ta yi hukunci, inda ta yanke wa Carlo Ancelotti zaman gidan kaso na shekara guda da tarar euro 386,361.
Sai dai duk da hukuncin, ba a sa ran Ancelotti zai yi zaman fursun. Kuma kotun ta wanke shi daga zargin laifukan haraji a shekarar 2015.
A cewar Reuters, a dokar Sifaniya ba a faye buƙatar waɗanda aka yanke wa hukuncin ƙasa da shekaru biyu kan laifin da ba na tarzoma ba. Amma dai lallai zai biya tarar da aka ɗora masa ta 386,361.
A halin yanzu dai Ancelotti mai shekaru 66 yana horar da ƙungiyar Brazil ne bayan ya bar Real Madrid a ƙarshen kakar bara.
Ba Carlo Ancelotti ne babban mai harkar ƙwallo da aka taɓa samu da lafukan haraji ba a Sifaniya. Taurari irin su Lionel Messi da Cristiano Ronaldo duka sun taɓa shiga matsala da hukumomin ƙasar lokacin suna wasa a Gasar La Liga
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
