Connect with us

News

Fiye Da Mutane 2,000 ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Watanni Shida A Najeriya  —NHRC

Published

on

Hukumar Kare Hakkokin Dan’adam ta Najeriya (NHRC) ta bayyana cewa ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga sun kashe mutum 2,266 a Najeriya cikin watanni shida na farkon shekarar 2025.

Wannan adadi ya zarce na dukkan shekarar 2024, inda mutum 2,194 ne suka rasa rayukansu sakamakon ayyukan ta’addanci da hare-hare a sassa daban-daban na kasar.

Advertisement

Tsadar Taki Ya Sa Manoma Sun Daina Noman Dawa Da Masara

A watanni shida na farkon shekarar 2024 kuwa, mutum 1,083 ne aka kashe.

A cewar Hukumar, wannan hauhawar adadin na nuna yadda matsalar rashin tsaro ke kara ta’azzara duk da kokarin da jami’an tsaro ke yi a fadin kasar.

Advertisement

A yankin Arewa maso Gabas, sojoji na ci gaba da fafatawa da ‘yan Boko Haram, yayin da a Arewa maso Yamma da Tsakiya kuma, ana fama da ‘yan bindiga da rikicin makiyaya da manoma. A Kudu maso Gabas kuwa, ana fama da matsalolin ‘yan aware.

A watan Yuni kadai, rahoton ya ce mutum 606 ne suka mutu a hare-haren da aka kai a wurare daban-daban na kasar.

Advertisement

Daga cikin su har da fiye da mutum 200 da aka kashe a harin da ‘yan bindiga suka kai a kauyukan Yelewata da Dauda a Jihar Benue.

Baya ga kashe-kashen, hukumar ta ce mutum 857 ne aka yi garkuwa da su a cikin watanni shida na bana, sabanin mutum 1,461 da aka sace a lokaci iri ɗaya a shekarar 2024.

Advertisement

Kazalika, rahoton ya bayyana yadda jami’an tsaro da ‘yan sa kai ke fuskantar barazana, inda aka kashe sojoji 17 a jihohin Kaduna da Neja, da kuma mambobin ‘yan bijilante fiye da 40 a jihar Zamfara.

 

Advertisement

 

TRT GLOBAL 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending