Connect with us

News

Sojojin Najeriya Sun Kama Masu Laifi 199, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda a Fagen Daga

Published

on

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 101 Sun Kama Wasu 182 A Cikin Mako Daya

Rundunar Sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun kama mutane 199 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihohi da dama, yayin da suka hallaka wasu ‘yan ta’adda a fagen fama.

Wani jami’i daga hedikwatar tsaro da ke Abuja ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa rundunar ta kara zage dantse wajen yaki da ta’addanci da inganta tsaro a sassan ƙasar.

NSCDC Ta Cafke Yaro Dan Shekara 15 Bisa Zargin Ajalin Wani Matashi A Jigawa

A jihar Borno, dakarun sojin 202 Battalion tare da hadin gwiwar ‘yan sa-kai na CJTF sun kai hari a garin Bama, inda suka tarwatsa wasu kayayyakin kungiyar ISWAP da JAS.

 

A jihar Sokoto kuwa, dakarun rundunar 8 Division Garrison sun gano wata hanya da ake amfani da ita wajen safarar miyagun ƙwayoyi, inda suka kama mutum huɗu tare da wasu kayayyaki.

A jihar Katsina, sojojin 17 Brigade sun kare wani hari da ‘yan bindiga suka kai wa rundunar ‘yan sanda, inda suka kwato wasu kayayyakin sadarwa da kuma kayan amfani.

Advertisement

A Warri da ke jihar Delta kuma, sojojin 3 Battalion sun kama mutane 183 da ake zargi da damfara ta yanar gizo, tare da kwace kwamfutoci 274 da wayoyin hannu 87.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da irin waɗannan ayyuka domin tabbatar da tsaro da murkushe ayyukan ta’addanci a ƙasar.

 

 

 

WIKKI TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending