Connect with us

News

Cutar Zazzabin Lassa Tayi Ajalin Mutane 151 A Najeriya – NCDC

Published

on

LASSA FEVER PIX

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta bayyana cewa adadin mutanen da suka rasu sakamakon cutar zazzabin Lassa a Najeriya ya kai 151 a cikin watannin farko na shekarar 2025.

A cewar wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Litinin ta hanyar shafinta na X, an tabbatar da mutum 800 da suka kamu da cutar daga farkon shekarar zuwa yanzu.

Sojojin Najeriya Sun Kama Masu Laifi 199, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda a Fagen Daga

Hukumar ta ce adadin mace-macen ya karu daga kashi 17.3 cikin 100 a shekarar 2024 zuwa kashi 18.9 cikin 100 a bana, abin da ke nuna yadda cutar ke kara kamari.

Sanarwar ta ce cikin sabbin rahotanni, an gano karin mutum 11 da suka harbu da cutar a jihohi shida, lamarin da ke kara yawan wadanda suka kamu da ita gaba daya a bana.

A cewar NCDC, jihohi biyar ne suka fi fuskantar barazanar cutar a bana, wadanda suka hada da Ondo, Edo, Bauchi, Taraba da Ebonyi, inda aka ce kimanin kashi 90 cikin 100 na masu dauke da cutar ke zaune.

Zazzabin Lassa dai na daya daga cikin cututtukan da ke yaduwa ta hanyar kashin beraye da kuma jini ko ruwa ko jikin mutum mai dauke da cutar, musamman idan ba a bi matakan kariya ba.

Advertisement

Hukumar ta bukaci jama’a da su kara kulawa da tsaftar muhalli, gujewa cin abinci ko sha ruwa daga wurare marasa tsafta, tare da kai rahoton duk wani wanda ke nuna alamun cutar cikin gaggawa.

 

 

 

TRT AFRIKA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending