Connect with us

News

Gwamna Uba Sani Ya Kaddamar Da Gidaje Ga Wadanda Rikicin ‘Yan Bindiga Raba Da Muhallansu A Jihar

Published

on

IDPs

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya kaddamar da gidaje da aka ginawa waɗanda rikicin ‘yan bindiga ya raba da muhallansu a jihar.

Gidajen, da ke cikin wani shiri na Qatar Sanabil Project, sun haɗa da makaranta, asibiti, kasuwa da kuma cibiyar koyon sana’o’i, kuma an gina su ne cikin haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Jihar Kaduna da Qatar Charity.

Advertisement

Cutar Zazzabin Lassa Tayi Ajalin Mutane 151 A Najeriya – NCDC

A bikin kaddamarwar da aka yi a ranar Litinin, Gwamna Sani ya bayyana wannan aikin a matsayin ɗaya daga cikin muhimman nasarorin gwamnatinsa, yana mai cewa hakan wani muhimmin mataki ne na farfado da rayuwar mutanen da rikicin ya shafa.

Gwamnan ya ce an gina makarantar ne domin ba da ilimi kyauta ga yaran waɗanda rikicin ya rutsa da su, da kuma samar da asibiti da cibiyar sana’o’i domin taimakawa al’umma gaba ɗaya.

Advertisement

Ya jinjinawa Qatar Charity bisa gudunmawar da ta bayar, tare da godewa Jakadan Qatar a Najeriya da Darektan ƙungiyar a ƙasar.

 

Advertisement

 

PEOPLES GAZETTE

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending