News
Majalisar Dattawa Ba Ta Amince Da Kirkiro Sabbin Jihohi Ba — Akpabio
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karyata jita-jitar da ke yaduwa a kafafen sada zumunta cewa Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da ƙirƙiro sabbin jihohi a Najeriya
Akpabio ya bayyana hakan ne a zaman majalisar na ranar Talata, yayin da yake mayar da martani ga wata sanarwa da Sanata Abdul Ningi ya gabatar, inda ya nuna damuwa kan yadda wasu ke ɗaukar batun kirkiro jihohi a matsayin abu da aka riga aka amince da shi.
Gwamna Uba Sani Ya Kaddamar Da Gidaje Ga Wadanda Rikicin ‘Yan Bindiga Raba Da Muhallansu A Jihar
Ya ce, “Majalisar Dattawa ba ta amince da wata sabuwar jiha ba. Abinda ke akwai shi ne, kwamitin duba kundin tsarin mulki ya karɓi sama da bukatu 42 daga sassa daban-daban na ƙasa, waɗanda ke neman a ƙirƙiro sabbin jihohi. Amma babu ko ɗaya daga cikinsu da ya kai matakin da doka ta tanada domin amincewa.”
Gwamna Uba Sani Ya Kaddamar Da Gidaje Ga Wadanda Rikicin ‘Yan Bindiga Raba Da Muhallansu A Jihar
Akpabio ya ja hankalin jama’a da kada su rinka gudanar da tarurruka ko shirye-shiryen goyon baya ga ƙirƙiro jihohi, yana mai cewa duk wani yunkuri da bai bi sahihin tsarin doka ba, to babu ingancinsa a gaban Majalisar.
Shugaban majalisar ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su rika sauraron hukumomin da suka dace wajen samun sahihan bayanai game da duk wani sauyi ko gyara da ya shafi kundin tsarin mulkin ƙasar.
-
News1 day ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
