Connect with us

News

NSCDC Ta Cafke Yaro Dan Shekara 15 Bisa Zargin Ajalin Wani Matashi A Jigawa

Published

on

Jami’an Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC) reshen Jihar Jigawa sun kama wani yaro mai shekaru 15 bisa zargin halaka wani matashi dan shekara 19 a kauyen Kafin Hausa da ke cikin ƙaramar hukumar Kafin Hausa a jihar.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Badaruddeen Tijjani, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse, babban birnin jihar, ranar Talata.

Majalisa Ta Amincewa Shugaba Tinubu Ya Ciyo Bashin Dala Biliyan 21

A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne a ranar Talata 16 ga watan Yuli, da misalin ƙarfe 11:30 na safe, lokacin da yaron wanda ake zargi ya kama mamacin, Barau Aliyu – mazaunin unguwar Beli – yana kiwon dabbobi a gonar mahaifinsa.

Tijjani ya ce, “Rikici ya barke tsakanin su yayin da yaron ya bukaci Barau ya fice daga gonar. Wannan ne ya kai ga amfani da sanda wajen bugunsa, wanda hakan ya haddasa masa munanan raunuka.”

An garzaya da Barau zuwa Asibitin Kafin Hausa, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa a rana ta biyu, da misalin ƙarfe 3:30 na rana.

Jami’in ya kara da cewa, bayan gudanar da bincike na farko, hukumar ta mika wanda ake zargin zuwa rundunar ‘yan sanda domin ci gaba da bincike da kuma yiwuwar gurfanar da shi a gaban kotu.

Advertisement

 

 

NAN

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending