Connect with us

News

Majalisa Ta Amincewa Shugaba Tinubu Ya Ciyo Bashin Dala Biliyan 21

Published

on

FB IMG 1753200680601

Majalisar Dattawan Nijeriya, a zaman ta na ranar Talata, ta amince da shirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na karɓar bashin ƙasashen waje da na cikin gida da ya kai jimillar dala biliyan 21.19, domin tabbatar da aiwatar da cikakken kasafin kuɗin shekarar 2025 da kuma shirin kasafin tsaka-tsakin lokaci (MTF).

Bashin da aka amince da shi ya ƙunshi rancen waje kai tsaye na dala biliyan 21.19 ($21.19bn), da Euro biliyan 4 (€4bn), da Yen biliyan 15 (¥15bn), da kuma tallafin kyauta na dala miliyan 65 ($65m). Haka kuma, gwamnatin za ta karɓi rancen cikin gida ta hanyar takardun bashi da za su kai Naira biliyan 757 (₦757bn), gami da wani shiri na tara dala biliyan 2 daga kasuwar cikin gida ta amfani da kayan aikin kuɗi da aka bayyana da kudin waje.

Ambaliya Ta Lalata Gidaje Fiye Da 100 A Zakirai

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Bashin Cikin Gida da na Waje, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya bayyana wa majalisar cewa buƙatar wannan bashi ta iso tun ranar 27 ga watan Mayu, amma aka samu jinkiri sakamakon hutun majalisa da wasu tsaiko daga Ofishin Gudanar da Basussuka na Ƙasa (DMO).

Sanata Wamakko ya ce, “Wannan shiri wani ɓangare ne na tsarin tattalin arzikin gwamnatin Tarayya na gina manyan ababen more rayuwa da farfaɗo da masana’antu da harkokin noma, domin ƙarfafa bunƙasar tattalin arziki da samar da ayyukan yi.”

 

A nasa bangaren, Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Dattawa, Sanata Olamilekan Adeola, ya bayyana cewa mafi yawan abubuwan da aka tanadar a cikin wannan bashi tuni an saka su cikin Tsarin Kuɗin Shiga na Tsaka-Tsakin Lokaci (MTF) da kuma kundin kasafin shekarar 2025, wanda hakan ke nuna muhimmancin amincewar majalisar domin tabbatar da aiwatar da dokar kasafin cikin lokaci.

Advertisement

Rahotanni na nuni da cewa gwamnatin na fatan amfani da wannan lamuni wajen kammala muhimman ayyuka da suka shafi gine-gine, wutar lantarki, noma, da hanyoyin sufuri, waɗanda ke da matuƙar muhimmanci ga ci gaban ƙasa da farfaɗo da tattalin arziki.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending