Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Dage Tsaftar Muhalli Na Watan Yuli

Published

on

Gwamnan Kano Abba Kabir Ya Yi Tafiya, Yayin Da Rikici Ke Ƙara Tsamari A Jami’yyar NNPP A Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta dage aikin tsaftar muhalli da ake gudanarwa a karshen kowane wata, inda ta ce ba za a yi aikin tsaftar watan Yuli ba.

Kwamishinan ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi na jihar, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar, Murtala Shehu Umar, ya fitar.

Advertisement

‎Wani Mutum Ya Mutu Yayin Da Yake Yunkurin Lalata Layin Wutar Lantarki Mai Ƙarfin 132kv

Sanarwar ta ce an dage aikin ne saboda bikin yaye dalibai na jami’ar Northwest da za a gudanar a ranar Asabar, wadda ta zo daidai da ranar da ake gudanar da tsaftar muhalli a jihar.

Kwamishinan ya ce duk da dagewar, ana sa ran ci gaba da gudanar da tsaftar muhalli kamar yadda aka saba a karshen watan Disamba mai zuwa.

Advertisement

Ya kuma bukaci al’ummar Kano da su ci gaba da kulawa da tsaftar muhallinsu a kullum, ko da kuwa ba a umarci kowa da tsaftar ba.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending