News
Shugaban Karamar Hukuma Ya Maka Gwamnatin Neja A Kotu
Shugaban karamar hukumar Chanchaga da ke jihar Neja, Alhaji Aminu Yakubu-Ladan, ya shigar da kara a kotun tarayya da ke Abuja, yana kalubalantar gyaran dokar da gwamnatin jihar ta yi, wanda ya rage wa’adin shugabannin kananan hukumomi da kansiloli daga shekaru hudu zuwa uku.
A cikin karar da aka shigar ranar 11 ga Yuli, wanda lauya Chris Udeoyibo ya gabatar da ita a madadinsa, Yakubu-Ladan ya nemi kotu ta duba da cewa dokar da jihar ke amfani da ita ta sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da kuma dokar zabe ta shekarar 2022.
Shugaban karamar hukumar ya bukaci kotun da ta dakatar da shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomi da aka tsara yi a ranar 1 ga Nuwamba, har sai an kammala wa’adin mulkin na shekara hudu da doka ta kasa ta tanada.
Ya kuma nemi kotu ta hana hukumar zabe ta kasa INEC da rundunar ‘yan sanda bayar da wani tallafi ko kariya ta tsaro domin gudanar da zaben.
Yakubu-Ladan na kalubalantar sashe na 29 (2) na dokar kananan hukumomi ta jihar Neja ta shekarar 2001, yana mai cewa ba ta da hurumin sauya wa’adin mulkin shugabannin kananan hukumomi ba tare da sabawa dokar kasa ba.
Sai dai kawo yanzu, ba a bai wa wani alkalin kotu wannan kara domin sauraro ba.
-
News23 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
