Connect with us

News

Kwamishinan Sufuri Na Kano Ya Janye Daga Karbar Belin Wanda Ake Zargi Safarar Miyagun Kwayoyi

Published

on

1753396125570

Kwamishinan Sufuri na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Namadi, ya janye matsayin da ya dauka na tsayawa beli ga wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a gaban kotu.

Sanarwar hakan na kunshe ne a wata takarda da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Abdullatif Auta, ya fitar a ranar Juma’a.

Advertisement

Shugaban Karamar Hukuma Ya Maka Gwamnatin Neja A Kotu 

A cewar sanarwar, Kwamishina Namadi ya rubuta wa kotu wasika yana bayyana aniyarsa ta janye belin da ya tsaya wa Sulaiman Aminu Danwawu, wanda Hukumar NDLEA ke tuhuma da laifin safarar miyagun kwayoyi.

Kwamishinan ya ce ya dauki matakin janye belin ne saboda dalilai na kashin kai da kuma bukatar kare mutuncinsa da martabar ofishin da yake rike da shi.

Advertisement

Ya ce lokacin da ya tsaya wa Danwawu beli, ya yi hakan ne saboda alakar jini da ke tsakaninsu da kuma jin kai, amma ba saboda yana marawa baya ayyukan da ake tuhuma da su ba.

“Bai kamata a dauki matakin da na dauka a matsayin goyon bayan safarar miyagun kwayoyi ba. Ni a shirye nake in mara baya ga duk wani kokari na gwamnati wajen yaki da shan kwayoyi da dawo da mutunci da tsaro a cikin al’umma,” in ji Kwamishina Namadi.

Advertisement

Ya kara da cewa yana da cikakken biyayya ga Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da gwamnatin jihar baki daya, tare da tabbatar da cewa zai ci gaba da bayar da hadin kai wajen dakile matsalar shan kwayoyi a jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending