Connect with us

News

An Cafke Basarake Bisa Zargin Taimakawa ‘Yan Bindiga A Katsina

Published

on

Jami’an tsaro a Jihar Katsina sun kama Dagacin Garin Sukutum da ke Karamar Hukumar Kankiya bisa zargin yana bai wa ‘yan bindiga bayanan sirri kan motsin jami’an tsaro da kuma al’ummomin yankin.

Majiyoyin tsaro sun shaida wa Zagazola Makama cewa an cafke basaraken ne bayan rahotannin leken asiri da suka danganta shi da kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke addabar yankunan Katsina.

Advertisement

Jami’an NDLEA Sun Kama Mutane 49 Da Ake Zargi Da Safarar Miyagun Ƙwayoyi A Kano

Rahotanni sun nuna cewa, ana zargin dagacin da yawan ziyartar maboyar ‘yan bindiga domin ci gaba da hulɗa da kuma tsara ayyukan ta’addanci tare da su.

Hukumar tsaro ta tabbatar da cewa wanda ake zargin yana hannun jami’anta, kuma ana ci gaba da bincike domin gano rawar da ya taka da kuma bankado sauran mutanen da ake zargin suna tare da shi a wannan harkar.

Advertisement

 

THE GUARDIAN 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending