Connect with us

News

Nasarar APC A Zaben Cike Gurbi Ta Tabbatar Da Sahihancin Mulkin Uba Sani – Maiyaki

Published

on

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya bayyana nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaben cike gurbi na kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya a mazabar Chikun/Kajuru a matsayin tabbacin amincewar al’umma da gwamnatin Gwamna Uba Sani.

Maiyaki, wanda ya yi jawabi ga manema labarai bayan sanar da sakamakon zaben mazabar Chikun/Kajuru da kuma Zariya Kewaye/Basawa, ya ce nasarar APC ta nuna irin goyon bayan da jama’a ke bai wa gwamnati da jam’iyya mai mulki.

Advertisement

Manchester ‎United Da Arsenal Za Su Fafata A Old Trafford

“A cewar sakamakon Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), jam’iyyar APC ta samu kuri’u 34,580 inda ta lallasa PDP wacce ta samu kuri’u 11,491, yayin da jam’iyyar ADC ta tashi da kuri’u 3,477, sai SDP da kuri’u 142,” in ji shi.

Kwamishinan ya bayyana wannan nasara a matsayin “na tarihi da kuma alamar karbuwa ga manufofin gwamnatin APC a Kaduna,” musamman a fannonin samar da ababen more rayuwa, inganta harkokin kiwon lafiya, gyaran makarantu da matakan tsaro.

Advertisement

Al’ummar Chikun, Kajuru, Zariya Kewaye da Basawa sun yi magana da murya daya – suna son shugabanci mai ci gaba, ba wai alkawuran siyasa marasa tabbaci ba. Sun nuna amincewarsu da salon jagorancin Gwamna Uba Sani na hada kan jama’a,” in ji Maiyaki.

Ya kara da cewa nasarar ta tabbatar da matsayin APC a jihar a matsayin babbar jam’iyyar siyasa, tare da karfafa matsayinta a kan turbar da ta dace kafin babban zaben 2027.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending