News
Gwamna Ya Kara Albashi Zuwa N104000, Likitoci Za Su Fara Karbar N582000
Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma, ya sanar da karin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan gwamnati a jihar zuwa Naira 104,000.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taro da ya gudanar tare da mambobin ƙungiyar kwadago na jihar a fadar gwamnati da ke Owerri.
‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Miji, Mata Da Kuma ‘Yarsu A Katsina
Haka kuma, an ƙara albashin likitoci a cikin ma’aikatan gwamnati na jihar zuwa Naira 582,000 a kowane wata.
Gwamna Uzodimma ya bayyana cewa wannan ƙarin albashi ya samu ne sakamakon ƙarin kudaden da jihar ke samu daga cikin gida da kuma ƙarin rabon da ake samu daga gwamnatin tarayya.
Ya jaddada cewa sabon tsarin albashin zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin jihar da kuma ƙara kwarin gwiwa da aiki tukuru a tsakanin ma’aikata.
Bugu da ƙari, Gwamnan ya sanar da ware Naira biliyan goma sha shida (N16bn) domin biyan bashin kuɗin fansho na tsofaffin ma’aikata a jihar.
