Connect with us

News

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Miji, Mata Da Kuma ‘Yarsu A Katsina

Published

on

yan bindiga sun sace mutane

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari a Filin Canada Quarters, Sabuwar Unguwa a cikin garin Katsina da misalin karfe 3:00 na asuba ranar Talata, inda suka sace mutum uku daga gida guda.

Wadanda aka sace sun hada da Anas Ahmadu, matarsa Halimat mai juna biyu da yarinyarsu Jidda.

Advertisement

Ambaliya Ta Lalata Gonakin Shinkafa 995 A Jigawa, Manoma Na Neman Dauki

Rahotanni sun ce wannan shi ne karo na farko cikin kusan shekaru biyu da irin wannan hari ya auku a cikin babban birnin Katsina.

A yayin harin, wani dan sa-kai mai suna Abdullahi Muhammad, mai shekaru 25, ya rasa ransa bayan da aka harbe shi yayin kokarin kare wadanda aka kai wa hari.

Advertisement

Majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan bindiga kusan bakwai ne suka shiga gidan, inda suka karya kofar shiga suka dauki wadanda aka sace.

Halimat dai diyar fitaccen dan kasuwace a jihar, Alhaji Usman Turare, wanda ya mallaki gidajen mai da dama.

Advertisement

Ana kyautata zaton burin masu garkuwar shi ne mahaifin matar, duba da irin arzikin da yake da shi.

Makwabta sun ce sun ji ‘yan bindigar suna magana a hankali, yayin da wani daga cikinsu ke musu jagora.

Advertisement

Kakakin ‘yan sanda a jihar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce DPO na yankin ya dauki matakan gaggawa domin dawo da zaman lafiya.

Har yanzu dai ba a tabbatar ko masu garkuwar sun bukaci kudin fansa ba.

Advertisement

 

 

Advertisement

WIKKI TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending