News
Ambaliya Ta Lalata Gonakin Shinkafa 995 A Jigawa, Manoma Na Neman Dauki
Ambaliya ta yi mummunar barna ga gonakin shinkafa sama da 995 a ƙauyuka 16 na mazabar Kuzunzumi da ke ƙaramar hukumar Babura, jihar Jigawa, lamarin da ake ganin zai iya jefa yankin cikin ƙarin matsalar abinci.
Rahotanni sun bayyana cewa, ambaliyar ta jefa daruruwan manoma cikin ƙaƙa-ni-ka-yi, inda yawancin su suka rasa dukiya da hanyoyin samun abinci.
NASSI, Nasarawa branch to Flag-up Empowerment program on 16th Sept. 2025
Mai magana da yawun al’ummomin da abin ya shafa, Abdurahman MaiKano, ya ce: “Wannan bala’i ya lalata gonaki tare da hanyoyin samun abinci, kuma ya bar iyalai da dama cikin ƙunci. Muna kira ga gwamnati ta kawo mana agaji cikin gaggawa.”
Ƙauyukan da aka fi samun barnar sun haɗa da: Kwagga/Martini, Fadibara, Kuzunzumi, Jikan Kanwa/Fulani, Dangaigai, Dankarda, Karfawa/Kanawa, Burukum Gari, Sabuwar Baka, Shashatu, Burukum Fulani da Kurtulla.
Wasu daga cikin manoman sun ce irin wannan bala’i na faruwa kusan kowace shekara, inda suka yi kira da gwamnati ta ɗauki matakan da za su dakile faruwar hakan a nan gaba.
Wani manomi, Suraja Muhammad, ya ce: “Muna fuskantar irin wannan bala’i duk shekara. Ya kamata gwamnati ta tuntuɓi masana don taimaka mana wajen hana sake faruwar wannan masifa.”
Shi ma wani manomi mai suna Musa ya bayyana cewa barnar ta shafi manyan gonakin shinkafa, wanda hakan zai iya haifar da tasiri a harkar abinci.
> “Barnar ta shafi manyan gonakin shinkafa. Wannan ba kawai zai rage kudin shiga manoma ba, har ma zai iya kawo matsalar abinci a ƙasa,” in ji shi.
A nata bangaren, hukumar ƙaramar hukumar Babura ta tabbatar da faruwar lamarin, inda shugaban ƙaramar hukumar, Hamisu Garu, ya tura tawaga domin duba yankunan da abin ya shafa tare da jajantawa al’ummar.
Jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar, Daudu Sulaiman, ya bayyana cewa“Ambaliyar ta yi mummunan lahani ga gonakin shinkafa kuma tana barazana ga samun abinci a yankin. Wannan na buƙatar matakin gaggawa.”
Al’ummar yankin sun ci gaba da roƙon hukumomin gwamnati da na agaji su kawo taimako cikin hanzari tare da ɗaukar matakan da za su kare faruwar irin wannan bala’i a nan gaba.
