News
Matar Aure Ta Kashe Kanta Bayan Samun Sabani Da Mijinta Kan Yadda Za A Auna Shinkafa
Wata matar aure mai shekara 17 mai suna Deola ta kashe kanta a kauyen Labi da ke ƙaramar hukumar Akinyele, Jihar Oyo, bayan wata rigima da ta yi da mijinta kan yadda za a auna shinkafa da za a dafa.
Deola, wadda ke da ɗa mai shekara ɗaya da watanni biyar, ta sha guba bayan mijinta, Seyi, ya shawarce ta da ta auna kofi biyu kacal, kasancewar shi ba zai ci abincin ba. Wannan ne ya haddasa musu sabani.
Wani Mai Tsaurin Ido Ya Sace Munduwar Fir’auna A Gidan Tarihin Masar
Bayan rikicin, mijin ya bar gida, yayin da Deola ta kai ɗanta makaranta. Sai daga baya ta sha maganin kashe ƙwari wanda ya haddasa mata amai. Duk da an garzaya da ita Asibiti amma ta rasu.
Lamarin ya tayar da hankulan al’ummar yankin, inda ake bayyana cewa ƙarancin juriya da rashin fahimtar juna a tsakanin ma’aurata na ci gaba da jawo mummunan sakamako.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta tabbatar da faruwar al’amarin, inda ta ce bincike ya na gudana.
