Connect with us

News

Jami’an ‘yan Sanda Sun Kama Sojan Bogi Da Masu Satar Mota Uku A Jigawa

Published

on

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Jigawa ta ce ta cafke wani mutum da ya ke yi wa kansa lakabi da soja tare da wasu mutane uku da ake zargi da satar mota, bayan da suka yi hatsari da motar da ake zargin sun sace a ƙauyen Sabon Sara, cikin Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa.

Mai magana da yawun rundunar, SP Shiisu Lawan Adam, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar ranar Laraba cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar 8 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 7:50 na safe.

Advertisement

‎Matar Aure Ta Kashe Kanta Bayan Samun Sabani Da Mijinta Kan Yadda Za A Auna Shinkafa

“Jami’an da ke ofishin Kafin Hausa sun kama mutane uku bayan sun yi hatsari da wata mota da ake zargin sun sace a Sabon Sara, Kafin Hausa LGA,” in ji shi.

Rundunar ta ce dukkan mutanen da aka kama mazauna jihar Kano ne. Sun haɗa da Kabiru Musa, mai shekara 35, ɗan unguwar Rimin Kebe, Umar Ali, mai shekara 25, ɗan unguwar Haye,Sabiu Bashir, mai shekara 25, ɗan garin Tokarawa.

Advertisement

Daga farko, Kabiru Musa ya bayyana kansa a matsayin Lance Corporal na Rundunar Sojojin 102 Guard Brigade da ke Abuja. Sai dai, bayan gudanar da cikakken bincike a Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) Dutse, rundunar ta gano cewa sojan bogi ne kawai.

A cewar sanarwar, an gano kayayyaki da dama a hannun waɗanda ake zargin, ciki har da katin ATM guda bakwai,lasisin tuƙi guda biyu, katin shaida na soja na bogi, da wasu abubuwa da ake zargin suna da alaka da ayyukan zamba.

Advertisement

Bayan kammala bincike, rundunar ta ce an riga an gurfanar da

mutanen a gaban kotu domin fuskantar shari’a.

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILY POST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending