Connect with us

News

‎Tallafin Barau Ya Ƙara Ɗaga Darajar Ci Gaban BUK – Shugaban Jami’ar ‎

Published

on

FB IMG 1758193309780 1200x1178

Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), Farfesa Haruna Musa, ya bayyana jin daɗin jami’ar bisa tallafin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibril, ya bayar domin ci gaban makarantar.

‎Farfesa Musa ya yi wannan jawabi ne a Abuja lokacin da ya kai wa Sanata Barau ziyarar ban-girma a majalisar dokoki.

Advertisement

Jami’an ‘yan Sanda Sun Kama Sojan Bogi Da Masu Satar Mota Uku A Jigawa

‎Ya ce jami’ar ta yaba da ƙudirin Sanatan na sabunta filin wasan kwallon ƙafa da ke sabuwar harabar jami’ar.

‎“Wannan aiki ya nuna sadaukarwa da kishin al’umma. Haka kuma al’umma za su ci gajiya da wannan ƙoƙari,” in ji Farfesa Musa.

Advertisement

‎Shugaban jami’ar ya ƙara da cewa suna yi wa Sanatan fatan Allah ya saka masa da alkairi tare da kuma albarka mai dorewa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending