Connect with us

News

Kashi 40 Cikin 100 Na ‘Yan Najeriya Na Fama Da Hawan Jini —  Kungiyar Likitoci

Published

on

FB IMG 1758238976878

Kungiyar likitocin zuciya ta Najeriya NCS ta nuna damuwarta yadda cutar hawan jini ke ci gaba da yaduwa inda take gargadin cewa kashi 40% na mutane na dauke da cutar a Najeriya.

Kungiyar ta fafi haka ne a taro Karo na 54 da take yi duk shekara domin tattauna hanyoyin inganta lafiyar zuciya.

Advertisement

‎Tallafin Barau Ya Ƙara Ɗaga Darajar Ci Gaban BUK – Shugaban Jami’ar ‎

An gudanar da taron ne tare da taron 17th Biennial Pan African Society of Cardiology (PASCAR) a karkashin taken “Hanyoyin rage farashin cutar cututtukan dake kama zuciya a Afrika”.

Da yake bada jawabinsa a wurin taron tsohon shugaban kungiyar NCS Okechukwu Ogah ya ce hawan jini na daga cikin manyan cututtukan dake wa gwamnatin Najeriya barazana.

Advertisement

“Hawan jini na daga cikin cututtukan dake yi wa mutane kisan farad daya a kasar nan.

“Muna da masaniyar cewa kashi 30% na mutane musamman wadanda suka dara shekara 15 na dauke da cutar wani binciken ya nuna cewa mutum kashi 40% ne ke dauke da cutar.

Advertisement

Ogah ya ce shugabancin da ya yi a Kungiyar NCS ya yi kokarin samar da bayanai kan yaduwar cututtukan dake kama zuciya.

Ya ce daya daga cikin mahimmancin abubuwan da kungiyar ta yi shine samar da takardar dake dauke da bayanai kan cututtukan dake kama zuciya da gwamnati za ta iya amfani da shi.

Advertisement

Ya ce kungiyar ta hada hannu da Gwamnatin Tarayya domin horar da ma’aikatan jinya kan Kula da masu fama da hawan jini a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko idan babu kwararren likita.

Hawan Jini a Najeriya

Advertisement

Hawan jini na daga cikin rukunin cututtukan da ba a yada su wato ‘Non communicable diseases NCD’ da ake da su a Najeriya sannan yana daga cikin cututtukan dake haddasa shanyewar bangaren jiki, bugawar zuciya, ciwon koda da kisa.

Bincike ya nuna cewa mutum kashi 30% zuwa 40% a Najeriya na fama da cutar inda da dama daga cikin su na dauke da cutar ba tare da sun sani ba.

Advertisement

Kungiyar Kiwon Lafiya na Duniya WHO ta ce cututtukan dake rukunin NCD kamar hawan jini, ciwon siga, ciwon daji, da cututtukan dake kama nunfashi na daga cikin cututtukan dake kashe sama da daya da kwatan mutane a Najeriya.

Masana sun yi gargadin cewa Najeriya na fuskantar annobar cutar hawan jini ta shuru saboda cutar ba ta da wata alama har sai an samu matsala mai tsanani.

Advertisement

Abin takaicin shine yadda masu fama da cutar basa samun kulan da ya kamata musamman yadda da dama daga cikin mutanen na dauke da cutar ba tare da sun sani ba.

Yawan cin gishiri, rashin motsa jiki, zukan taba sigari, Shan barasa giya na daga cikin hanyoyin kamuwa da cutar.

Advertisement

Karancin asibitoci da tsadar magunguna duk suna cikin matsalolin da masu fama da cutar ke fama da su.

 

Advertisement

 

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending