Connect with us

News

Kasar Albania Ta Naɗa Mutum-mutumi Na AI A Matsayin Minista

Published

on

Ministar AI a Albania

Kasar Albania ta naɗa mutum-mutumi na fasahar AI a matsayin minista – abin da ake ganin shi ne karo na farko a tarihin duniya.

Mutum-mutumin mai suna Diella, wacce kalmar ke nufin “rana” a harshen Albania, ta bayyana a gaban majalisar dokokin ƙasar a ranar Alhamis inda ta gabatar da jawabi.

Advertisement

Kashi 40 Cikin 100 Na ‘Yan Najeriya Na Fama Da Hawan Jini —  Kungiyar Likitoci

A cikin jawabin nata, ta ce ba ta zo don ta maye gurbin ɗan Adam ba, sai dai don taimaka masa.

“Wasu na cewa ba na kan kundin tsarin mulki saboda ni ba mutum ba ce. Amma babban hatsari da kundin tsarin mulki ke fuskanta ba injuna ba ne – sai dai masu mulki.”

Advertisement

Firaministan ƙasar, Edi Rama, shi ne ya naɗa Diella a makon da ya gabata. Ya ce za ta kula da dukkan al’amuran kwangiloli na gwamnati domin a kawar da cin hanci, kuma a tabbatar da gaskiya da bayyana duk kuɗaɗen gwamnati da ake kashewa.

An fara ƙaddamar da Diella a watan Janairu a matsayin wata na’urar AI da ke taimaka wa jama’a wajen amfani da dandalin e-Albania, wato dandali na yanar gizo da ke bayar da takardu da ayyuka na gwamnati.

Advertisement

Wannan mataki ya jawo martani daga masana da al’umma. Wasu na ganin hakan wani sabon salo ne da zai iya kawo sauyi a tsarin mulki da gudanar da gwamnati, yayin da wasu ke nuna damuwa kan tasirin injina ga makomar ayyukan ɗan Adam.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending