Connect with us

News

Dalibi Ya Shafa “Super Glue” A Idanun Abokansa 8 Yayin Da Suke Barci

Published

on

file 00000000d4f0622fb3b36d6db08a9c95

Akalla dalibai takwas sun kwanta a asibiti a jihar Odisha ta gabashin Indiya, bayan wani ɗalibin Makarantar Kwana ya shafa musu mannewar “super glue” a idanunsu yayin da suke barci.

Lamarin ya faru ne a daren Juma’a a makarantar kwana da ke ƙauyen Salaguda, gundumar Kandhamal, kimanin kilomita 248 daga Bhubaneswar, babban birnin jihar.

Jama’a Sun fi Yadda Da Neman Magani A Shagunan Chemist Fiye Da Zuwa Asibiti Domin Ganin Likita

Rahotanni sun nuna cewa daliban da abin ya faru da su sun farka da idanunsu a manne, suna kuka, yayin da likitoci ke ƙoƙarin cire musu mannewar da ta haɗe gashin ido da fatar ido.

“Likita sun tabbatar da cewa mannewar ta haifar da matsananciyar illa a idanun yaran, amma daukar matakin gaggawa na likita na iya taimakawa wajen kauce musu rasa gani gaba ɗaya,” in ji rahoton.

Hukumomi sun kafa kwamiti na musamman domin gudanar da bincike kan abin da ya faru.

A halin yanzu kuwa, an dakatar da shugaban makarantar bisa gazawa wajen kula da ɗaliban.

Advertisement

 

Xinhua/NAN

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending