Connect with us

News

SSANU Da NASU Za Su Tsunduma Yajin Aiki

Published

on

SSANU NASU

Kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i da ba malamai ba (NASU) da na manyan ma’aikatan jami’o’i (SSANU) sun bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwana bakwai kafin su tsunduma yajin aiki.

Kungiyoyin sun ce gwamnatin ta gaza cika alkawuran da ta dauka, ciki har da biyan alawus, albashin da aka rike, karin albashi, da kuma sabunta yarjejeniyar da aka kulla tun shekarar 2009.

Dalibi Ya Shafa “Super Glue” A Idanun Abokansa 8 Yayin Da Suke Barci

A cewar shugabannin kungiyoyin, tun a watan Yuni ne suka rubuta wasika ga ma’aikatar ilimi, lamarin da ya kai ga taro a watan Yuli. Amma duk da kafa kwamiti domin duba batun rabon kudin alawus na N50bn, ba a ga wani ci gaba ba.

“Mun yi hakuri, mun yi rubuce-rubuce, amma gwamnati ta yi shiru. Saboda haka, daga ranar Litinin, 15 ga Satumba, 2025, muna bai wa gwamnati kwana bakwai don ta cika alkawura. Idan ba haka ba, za mu fara yajin aiki,” in ji wasikar da kungiyoyin suka aika wa ministan ilimi.

Kungiyoyin sun ce idan suka shiga yajin aiki, jami’o’i da cibiyoyin ilimi a fadin kasar za su rufe, abin da zai sake kawo tsaiko ga harkar karatu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending