Connect with us

News

Farashin Gas Ya Yi Tashin Gwauron Zabi A Kano

Published

on

Mazauna birnin Kano sun bayyana ƙorafi da damuwa kan yadda farashin gas ɗin girki (LPG) ke ƙara tashin gwauron zabi, tare da ƙara tsananta karancin samunsa a kasuwa, lamarin da ke jefa su cikin ƙalubale wajen gudanar da ayyukan yau da kullum.

Advertisements
Advertisements

Rahoton da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya tattara a ranar Laraba ya nuna cewa, tashoshin sayar da gas da dama sun ƙare da kayayyaki, yayin da waɗanda ke buɗe kuma suke aiki ke cika da dogayen layukan masu saye.

Advertisements

Ƙungiyar SSANU Da NASU Za  Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

A cikin kwanaki biyar kacal da suka gabata, farashin gas ya ƙaru da kusan kashi 25%, inda kilogram ɗaya yanzu ke sayarwa tsakanin N1,800 zuwa N2,000, sabanin tsohon farashin da yake N1,200.

Advertisements
Advertisements

Haka kuma, cikon gas mai nauyin 12.5kg yanzu ya kai tsakanin N20,000 zuwa N25,000, sabanin N14,000 da ake biya a baya — lamarin da ya ƙara ɗora wa al’umma matsin tattalin arziki a lokaci da rayuwa ke ta tsada a sassa daban-daban naƙasar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending